|
|
|
|
| |||
|
Daga: Sheikh Saleh Zaria salehzaria@al-aazam.org ________________________ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Wannan
makala ce a
Da farko
yana da kyau a fahimci cewa Ahlul-bait (A.S) duk abu daya ne. 'Ya'yan babban
bishiyar nan ce ta Sakon Allah, wadda da ta yi rassa a tarihin dan Adam
tun farkon duniya, ta yadu ta hanyar Annabawa (AS), ta bunkasa a kan Manzo
(SAWA) da mataimakinsa Imam Ali (AS), sannan ta fitar da nunannun 'ya'ya su ne
tsarkakan Imamai daga Ahlul-baiti (AS). Imamai (AS) wanzajjen hasken Allah ne a
doron kasa, masu haskaka duniya da samuwarsu. Don haka ko da Imami bai ce uffan
ba a cikin al'umma, samuwarsa kawai hujja ce ga talikai; "Ba don Hujja ba
da an shafe kasa da abin da ke cikin ta" (Hadisi).
Don
bayanin wannan hakika ne ma daya daga cikinsu (Imam Ali A.S) yake cewa:
"Su (Ahlul-Baiti) ne rayuwar ilimi, kuma mutuwar jahilci, hakurinsu na ba
ku labarin iliminsu, zahirinsu na nuna muku abin da suka boye, shirunsu na
Daga
abin da ya gabata za a iya fahimtar cewa a tushe babu wani bambanci a
Hukuncin
Allah da hikimarSa sun hukunta zabawa Imam Hussaini mafi wahalar hanya da ta
bambanta da ta sauran Imamai (AS). Hanyar da ta bukaci sadaukar da 'ya'ya da
dangi, da mikawa mutuwa zababbun makusanta da masoya, da shahada ta mafi
wahalar hanya tattare da wahlahlu da masifu. Wannan na daya daga cikin dalilan
da suka sa Manzo ya kebe kulawa ta masamman ga Imam Hussaini (AS).
An
riwaito cewa a ranar da aka haifi Imam Hussain (wanda ya dace da ranar 3 ga watan
Sha'aban, shekaru uku bayan hijira), Manzon Allah (SAWA) ya tarbe shi da dariya
da kuka a hade! Sai Asama'u ta tambaye shi dalilin kukansa cikin mamaki, sai y
ace mata: "Azzalumar kungiyar nan za ta kashe shi a baya na, kar Allah Ya
hada su da cetona." (
E'
dariyarsa (SAWA) ta murnar haifar masa wannan jika mai albarka ne. kukansa
kuwa, na wahalhalun da zai shiga ne; in ka so ka ce, na tsanantar hanyar
aikinsa ne!! Don haka ne ma muke cewa ai Manzo ne farkon wanda ya fara kuka da
nuna tausayin Imam Hussaini bisa abin da zai same shi a
Don haka
a yunkurin Imam Hussain a kwai darasin kuka da tausasa zuciya. Wannan shi ne
abin da zan yi magana a kai nan gaba insha'Allah.
Allah Ya
sada mu da alheri.
Bissalam
Saleh
Zaria |
||||